September 17, 2026

Sayyada Nusaiba Ta Shirya Taron Bikin Maulidin Annabi S.A.W A Kano

IMG-20250915-WA0147

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Sabuwar Jaruma, kuma mawakiyar Annabi Nusaiba Ya’u (Nusy) ita ma ba a bar ta a baya ba wajen shirya taron bikin Mauludin Manzon Allah S A W domin nuna farin ciki da zagayowar ranar haihuwasa .

Don haka ta shirya wani gagarumin taron bikin Mauludin don bayar da ta ta gudummawar wajen nuna soyayyar ta ga Manzon Allah S A W.

A ranar Juma’a 18 ga Rabi’ul Awwal 1447 wanda ya yi daidai da 12 ga Satumba 2025 ne dai aka gudanar da taron bikin Mauludin a layin Madugu gidan Oga Ya’u dake Unguwar Gwamaja a cikin garin Kano.

Taron Mauludin wanda aka fara tun daga karfe 7 na dare har zuwa wayewar gari, ya samu halartar manyan Sha’irai da kuma Jarumai daga Kannywood.

An dai yi karatun Al’kur’ani tare da ziyarorin Manzon Allah S A W da kuma wakokin Yabo a wajen. Kazalika Malamai da suka halarci wajen sun yi nasiha a kan muhimmancin riko da sunnar Manzon Allah S A W.

Bayan ƙasida da ta gabatar a wajen shugabar shirya taron Sayyada Nusaiba Ya’u (Nusy), ta nuna farin cikin ta ga jama’ar da suka halarci wajen taron nata , in da take cewa ” Duk da taron Mauludi ne kowa yana zuwa don nuna soyayyar sa ga Manzon Allah S A W , to gaskiya an yi mata kara da aka amsa gayyata ta da aka yi.

Saboda haka ta yi wa kowa fatan alheri, Allah ya kara mana son Manzon Allah S A W, da kuma yin koyi da shi”

Nusaiba Ya’u ( Nusy) dai sabuwar Jaruma ce da ta fito cikin finafinai da suka hayda da Rayuwar Matasa, Aminiyata da sauran su.

Baya ga haka mawakiyar Annabi ce da ta yi ƙasidu masu yawa.

‘Yan fim dai da dama, sun halarci wajen, kaɗan daga cikin su akwai Bashir Bala Ciroki da Hajiya Fati Kuntau Kilishi a cikin fim din Labarina Hauwa Ahmad da sauran su.

About The Author