September 17, 2026

Abinda Ya Sa Na Shirya Kasuwar Baje-Kolin Littattafai. Cewar Kabiru Jammaje

IMG-20250719-WA0021

Abinda Ya Sa Na Shirya Kasuwar Baje-Kolin Littattafai Cewar Kabiru Jammaje

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A ranar 27 ga Yunin da ya gabata ne aka ci kasuwar rana guda ta Bajekolin Littattafai ko Gwanjo wanda.fitaccen Malamin turanci Malam Kabiru Musa Jammaje ya shirya wanda dunbun Jama’a Malamai da kuma daliban ilimi suka halarci wajen Bajekolin Littattafan domin sayen Littattafan Wanda aka sayar da su cikin farashi mai sauki.

Wani abin burgewa kasuwar Bajekolin Littattafan ta tsawon wuni guda ce da aka shirya za a Bajekolin Littattafai sama da 450 domin sayarwa ga masu bukata.

To sai dai kasuwar ta ci ta cinye a kasa da sa’o’i uku na fara Bajekolin, inda mutane daga ciki da wajen Kano suka yi taron cikar Kwari a wajen Bajekolin dake tsohon Ofishin Jammaje na Shatale talenTal’udu suka saye Littattafan.

Wasu daga cikin litattafan da aka Baje-Kolin su

Bayan kasuwar Bajekolin ta ci ta watse ne wakilin mu ya nemi jin ta bakin Malam Kabiru Musa Jammaje a game da manufar shirya taron Bajekolin.

Malam Kabiru Musa Jammaje ya ce

“To shi dai wannan taron na Bajekolin ko Gwanjon Littattafai da na shirya . Idan za ka iya tunawa a kwanakin baya an yi wata muhawara tsakanin Farfesa I B K da Dakta Bala Muhammad, a kan maganar karance karance ko a jikin Allo ko ta hanyar Littattafai.

To wannan muhawa da aka yi ta fitar da sako mai karfi ga al’umma na cewa ya zama dole a tashi a rungumi karance karance. Kuma bayan da aka yi wannan muhawa ne na samu wani ilimi na kwaso Littattafai na da na yi amfani da su na yi Gwanjon su ta hanyar Bajekolin su, kuma na sayar da su cikin farashi domin su ma Al’umma su amfana.

Kuma su wadannan Littattafai ne da na rinka tattarawa a kasashen waje na sayo su da yawa na karanta su. Don haka na ga bai kamata na yi ta ajiyar su ba, kuma ga masu bukata suna nema. Duk da cewar wannan Littattafan ba su fi kashi 30 cikin 100 na Littattafai da nake da su ba, na dai kwaso kadan ne daga ciki.

 

Wani ɓangaren wasu littattafan da aka kawo domin Baje-Kolin su a wajen taron

Da yawa akwai wadanda suka yi tunanin ko Littattafan da ka wallafa ne za ka yi Bajekolin su sai kuma aka ga wasu ne daban.

Ai daman kamar yadda muka sanar musamman a Soshiyal Midiya mun fadi cewa Littattafai na cikin gida da na kasashen waje. To ka ga tun da na ce har da na kasashen waje bai kamata mutane su dauka cewar Littattafai na ba ne kawai. Don a cikin Littattafan da aka yi Gwanjon su wanda na wallafa biyu ne ko uku.

Kuma dai ka ga Littattafan da aka kawo sun kai sama da 460, kuma kusan dukkan su na kasashen waje ne, don haka da yawa mutane sun san cewa ba Littattafai ne da na rubuta ba, kamar dai yadda na dauki hoton su na nuna a Soshiyal Midiya, don haka mutane sun san me za su gani.

A sanarwar dai an nuna za a yi Bajekolin daga sha biyu zuwa bakwai na yamma, sai kuma kasuwar ta ci ta kare a kasa da sa’o’i uku aka kammala.

To nima dai abin da ya ba ni mamaki kenan, don mun shirya za a Kai yamma din, amma sai ya zamana an Fara sha biyu, amma a cikin minti 30 aka saye kusan rabin Littattafan don haka sai ya zama ba za mu kai yamma din ba saboda kaso 90 cikin 100 na Littattafan sun kare

Kuma gaskiya na ji dadi sosai da Jama’a suka amsa kiran, kuma babu abin da zan ce wa mutane musamman abokaina na Facebook sai godiya.

Tun da a Facebook ne na tallata taron Bajekolin kuma mutane suka taya ne Jama’a suka gani suka zo suka sai saya, wanda hakan ya nuna suna son karance karance, suna son ilimi, kuma suna son su ci nasara a rayuwa. Kuma Alhamdulillah mu kan mu mun cimma nasarar abin da muka tsara na shirya kasuwar Bajekolin.

Ko akwai wani lokaci nan gaba da ake tunanin za a kara yi tun da an samu nasara?

To gaskiya ba zan iya cewa ga Lokacin da za a kara yi ba, saboda wannan Littattafai ne da aka dade ana tara su, don wasu na sayo su a Indiya wasu a Afirka ta Kudu wasu a Kenya da Ingila, duk ga su nan dai Littattafai ne kala kala da aka dade ana tara su, don wasu za ka ga na saye su tu 2010 zuwa yanzu, don haka babu wata ranar da za ka ce za ka Kara yi sai dai idan lokaci ya bayar da a kara yi.

Su wadannan Littattafai da yawa masu sayen su sun shaida mana sun dade suna neman su ba su samu ba a kasuwanni, ko yanayin farashin ya yi sauki kenan?

Wato daman abin da na yi duba da shi kenan. Na farko dai su Littattafan nan masu kyau ne na asali ba kwafi ba, na samo su ne daga kamfanonin da suka buga su. Sannan kuma ba Littattafai ne da za ka iya samun su a kasuwar mu nan kai tsaye ba , don haka sai suka kasance cikin sauki kuma za ka same su ba tare da ka sha wahala ba, don mafi yawan su sai ka je kasashen waje za ka iya samun su, don haka ka ji ko wandanda suka zo saya din abin da suke ta fada kenan.

Sai ka ji wani ya ce ya yi shekaru yana nema bai samu ba. Kuma Littattafan da za ka saya dubu biyar a nan, idan a kasuwa ne sai dai ka yi maganar dubu ashirin, don mun yi sauki ne na kashi hamshin cikin dari ko ma sama da hakan, don babu Littattafai da ya wuce dubu biyar a cikin wadanda muka sayar, don haka wani saukin da muka yi ya kai na kashi tamanin cikin dari .

Don haka ina kara godiya ga dukkan Jama’ar da suka halarci taron Bajekolin da Dalibai na da sauran Jama’ar da suka zo don mutane da yawa na dade ban gan su ba sai a wannan lokacin, don haka wannan Bajekolin ya zama kamar wani taron sada zumunci tsakani na da Masoya da Dalibai na musamman tsofaffin da suka kammala makarntar Jammaje Actually a baya, sun nuna Mana su ‘yan halak ne sun yi mana kara sun zo da yawa.

Ina godiya sosai Allah ya saka da alheri Allah ya bar zumunci.

To Madalla mun gode.

Nima na gode sosai.

About The Author