Jami’ar Fasaha Ta Lafiya Ta Tarayya Ta Tsafe Za Ta Fara Aiki Nan Ba Da Jimawa
Daga Hussaini Yero
Sabuwar Jami’ar gwamnatin tarayya ta fasahar kiwon lafiya ta Tsafe da ke cikin Jihar Zamfara,za ta fara aiki nan ba da jimawa ba.Sanata Ikira Bilbis Mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya a Majalisar Dattawan ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.
Sanata Ikira ya ce ana kan kammala dukkan wasu batutuwa da suka dace da kuma tsare-tsare domin ganin Jami’ar ta fara aiki gadn-gadan”.
“Ya ce gwamnatin jihar Zamfara Karkashin Jagorancin gwamna Dauda Lawal ta ba da wuri na wucin gadi wanda shi ne wurin dindindin na kwalejin kimiyyar lafiya ta Tsafe mallakar Jihar.domin fara karatu a cikinta.
Ya kuma ce nan ba da dadewa ba,Hukumar kula da jami’oin zasu turo Mataimakin Shugaban Jami’ar da Manyan Ma’aikata dan fara aiki a sabuwar Jami’ar gadn-gadan.
Sanata Ikira, Ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa goyon bayan kafa jami’ar domin samar da kwararrun ma’aikata a fannin kiwon lafiya a fadin kasar nan.
Sanata Bilbis ya kuma yabawa gwamna Dauda Lawal bisa samar matsugunin wucin gada da Jami’ar zatafara
