September 17, 2026

PDP Na Ƙara Samun Koma Baya Inda Tsaffin ‘Yan Takara 267 Suka Sauya Sheƙa a Katsina .

FB_IMG_1750401151897

PDP Na Ƙara Samun Koma Baya Inda Tsaffin ‘Yan Takara 267 Suka Sauya Sheƙa a Katsina .

Zuwa yanzu dai jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina na cigaba da fuskantar tawaye daga ‘ya ‘yan ta domin shiga sabuwar haɗaka da za a tunkari jam’iyya mai mulki a jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.

Wannan sabuwar tafiya ƙarƙashin tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Inuwa na cigaba da zama barazana a cewar masana siyasa idan har an samu daidaito a matakin ƙasa

Kamar yadda suka bayyana tsaffin ‘yan takara da suka haɗa da waɗanda suka yi takarar majalisar jihar a zaɓen 2023 mutum 25 daga cikin talatin 34 a ƙarƙashin jam’iyar PDP

Sai kuma mutum 13 da suka takarar kujerun shugabannin ƙananan hukumomi a zaɓen da ya gabata na shekarar 2025 tare da Kansiloli 225 daga cikin 361 da suka yi takarar a zaɓen 2025

Jagoran wannan sabuwar tafiya kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa ne ya bayyana haka a lokacin da tsaffin ‘yan takarar suka je ofishin sa domin jadadda goyon bayan su akan sabuwar tafiya.

Shima da yake magana a madadin sauran ‘yan takarar majalisar dokokin jiha a zaɓen 2023 Hon. Jamilu Yahaya ya bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar PDP ne saboda yadda aka nisantar da su daga al’umma wanda su ne ke yin zaɓe.

Ya ƙara da cewa tattaunawa ta yi nisa tsakanin su da shugabannin sabuwar tafiya wajen haɗa hannun domin tunkarar jam’iyya mai mulki tare da tabbatar da sun kai ta ƙasa a 2027

A nashi ɓangaren shugaban ‘yan takarar shugabancin ƙananan hukumomi Hon. Yasir Ibrahim ya ce sun shiga wannan haɗaka ne saboda irin yaudarar shugabanci da aka yi masu a tsohuwar jam’iyyar PDP da ke fama da rikice-rikice

Ya ƙara da cewa zuwa yanzu ‘yan takara 13 na shugabannin ƙananan hukumomi sun shiga wannan tafiya a ya yin da ake cigaba da tattaunawa da sauran domin haduwa waje guda

Da yake nasa tsokaci shugaban tsaffin ‘yan takarar Kansiloli na jam’iyyar PDP a zaɓen da ya gabata Hon. Usman Aminu ya bayyana cewa su 225 ne suka amince da wannan sabuwar tafiya, amma yana ƙoƙarin ganin sauran ma sun shiga an yi da su.

About The Author