September 18, 2026

Yadda Hukumar Saka Hannun Jari Ta (KIPA) Ta Shirya Taron Wayar Kai Ga Masu Ƙananan Sana’o’i A Daura 

IMG_8453

Hukumar Saka Hannun Jari ta jihar Katsina Ta shirya taron wayar da Kai Ga ƙananan ‘Yan kasuwa domin su amfani da basusukan da gwamnati ke badawa a garin Daura ta jihar Katsina

Shirya wannan taro na da nufin yin jagoranci ga ƙananan yan kasuwa da kungiyoyin yan kasuwa domin su fahimci tsare-tsaren karbar basusukan da ake badawa don su bunƙasa kasuwanci su.

Taron wanda aka shirya shi, a Daura da nufin samar da wata sahihiyar hanya da zata taimakawa ƙananan yan kasuwa su samu basusukan da gwamnati ke badawa domin haɓaka harkar kasuwanci a jihar Katsina.

Baya ga Hukumar saka hannun jari da ta shirya taron akwai hukumomi guda biyar da suka haɗa da bankin Manoma da bankin yan kasuwa da Hukumar bunƙasa ƙananan sana’o’i ta KASEDA da NIRSAL da kuma bankin Jaiz da sauran hukumomi duk sun gabatar da jawabai ga mahalarta taron.

Tunda farko da yake nasa jawabin shugaban hukumar saka hannun jari na jihar Katsina Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana cewa sun zo Daura ne domin a faɗakar da al’umma musamman ‘yan kasuwa don su amfana da basusukan da gwamnati ke badawa wanda ba ruwa a cikin sa.

Ya ƙara da cewa harkar kasuwanci ce kaɗai mafita a wannan lokaci, ba wai dogaro da gwamnati ba, idan har masu ƙananan kasuwanci za su yi amfani da bashin da hukumomi da bankuna ke haɗawa lallai za su bunƙasa kasuwancin su a jihar Katsina da ƙasa baƙi ɗaya

Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi wanda ya ce al’umma na cigaba ne kawai idan ta ɗauki harkar saye sayarwa da mahimmanci amma ba dogaro da gwamnati ba, ya ƙara da cewa duk ƙasashen da suka ci-gaba sun ɗauki kasuwanci da mahimmancin gaske.

Tunda farko da yake jawabi mataimakin gwamnan jihar Katsina Malam Faruƙ Lawal Jobe wanda ya samu wakilcin babban sakataren a ofishinsa, Alhaji Mannir Aliyu Mani ya bayyana cewa gwamnati mai ci yanzu ta yi nata aikin saura su al’umma ya ragewa akan bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana’o’i

Ya ƙara da cewa, a jihar Katsina ba a taɓa gwamnatin da ta zo da tsare-tsaren da za su taimakawa ƙananan yan kasuwa ba kamar gwamantin Malam Dikko Umar Raɗɗa ba.

‘Ko cikin wannan satin an baiwa mata 500 jari bayan an ba su horo domin su gudanar da ƙananan sana’o’i wanda gwamantin jihar ta shirya ta ɗauki nauyi domin ta taimakawa masu ƙananan sana’o’i a fadin jihar Katsina.” inji shi

Alhaji Mannir Aliyu Mani ya ƙara da baban burin wannan gwamanti shi ne ta ga al’umma sun tsaya da kan su ta hanyar bunƙasa kasuwanci su ba wai dogaro da gwamnati ba, kamar yadda aka ɗorawa al’umma akan wannan tunanin a baya.

Wakilin mataimakin gwamnan yana mai cewa wannan gwamnati tana da tsare-tsare masu yawa da suka shafi bada tallafi da kuma bashi Wanda ba ruwa domin ganin masu ƙananan masana’antu sun tsaya da ƙafarsu.

Daga cikin waɗanda suka yi jawabai akwai wakili daga hukumar bunƙasa kananan sana’o’i ta jihar Katsina KASEDA da kuma Bankin BOA da BOI Da NIRSAL da bankin Jaiz da sauran hukumomi ga mahalarta taron da suka haɗa maza da mata

About The Author