September 17, 2026

Gwamnatin Tinubu ta aiwatar da sabon tsari da ya fara farfaɗo da darajar Naira. 

IMG-20241211-WA0014

Gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar da sabon tsari da ya fara farfaɗo da darajar Naira.

A karshen watan Nuwamba da ya gabata, Dalar Amurka ta kai N1,672.69 zuwa N1,730, tsakanin farashin CBN da na kasuwar bayan fage, amma a yanzu, dalar ta karya zuwa N1,525 wanda ya kai kusan kimanin kashi 10 cikin ɗari.

Wannan ya samu ne sakamakon sabon tsarin EFEMS da gwamnatin Tinubu ta ƙirƙiro dan samar da daidaito da kuma sanya idanu akan hada-hadar kuɗaɗen waje a Najeriya.

Yaya wannan tsarin yake?

Tsarin EFEMS wato (Electronic Foreign Exchange Matching System) tsari ne da CBN ta samar da shi da ya kawar da tsohon tsarin da ake kai na AFEM wato (Autonomous Foreign Exchange Market.

Kamar yadda ma’abota siyan Dollar suke yi a tsarin P2P dake kan Binance, kowa zai iya sanya farashin da yake siyan Dollar ko kuma ya Siyar, zaɓi ya rage ga wanda zai siya ya zaɓi inda ta fi sauƙi ya saya a ƙarƙashin kulawar Binance.

Kwatankwacin haka wannan tsarin na EFEMS yake, bankuna za su sanya farashin su akai, masu siya sai su zaɓi su siya daga farashi mafi sauƙi ƙarƙashin kulawar CBN.

Hakan ya sa farashin Dalar samun daidaito saɓanin tsarin baya na AFEM da kowanne banki zai sanya farashin da ya ga dama ba tare da kulawar CBN ba, kuma saidai mai son siya ya siya a haka muddin a nan bankin yake son siya, babu zaɓin neman sauƙi daga wani wajen ta bankin ka ko da farashin su ya fi sauƙi akan bankin ka.

A yanzu dukkan bankuna suna kan wannan tsarin na EFEMS, kuma nan da lokaci kaɗan zai haɗe dukkan kamfanonin canji da suke da lasisi a faɗin ƙasar, hakan zai tsayar da farashin dollar ya zama bai ɗaya tare da samun sauƙin tashin ta da ake samu a baya da kuma kulawar yadda ake hada-hadar kuɗin daga CBN.

Wani abu da gwamnatin tarayyar ta ƙara yi shi ne, tayi ƙoƙarin samar da hannun jari daga ƙasashen ƙetare wanda hakan ya sanya yawaitar Dalar a Najeriya wanda zai cigaba da rage farashin ta da ɗaga darajar Naira, sai kuma ƙaruwar kuɗaɗen haraji da ƙasar ke samu daga mai, da kuma sababbin tsare-tsaren inganta tattalin arziƙin ƙasar ta ɗabbaƙa.

About The Author