September 18, 2026

Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Da Mulki (KSITM) Zata Shirya Taron Ƙasa Da Ƙasa Akan Kirkiran Zamani (AI) A Katsina

0
FB_IMG_1733209618774

Kwalejin Kimiyya da fasaha da sha’anin mulki ta KSITM zata shirya taro irin sa na farko akan kirkiri zamani (AI) da lissafi a Katsina

Taron dai zai kasance irin sa na farko da wannan kwaleji zata gudanar tun bayan kafa ta kusan shekaru goma da suka gabata inda ake sa ran masana daga ɓangarori daban-daban na ilimi za su halarci taron.

Shugaban hukumar gudunmawar kwalejin Dakta Muttaƙa Rabe Darma ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala taron hukumar gudunmawar karo na farko tun bayan ba su wannan muƙami.

A cewar sa, ana sa ran za a gudanar da wannan taron a watan Afrilun 2025 tare da hadin gwiwa da jami’ar Musulmi ta Alƙalam da ke Katsina da kuma hukumar yada labarai ta jihar Katsina.

Ya ƙara da cewa, hukumar gudunmawar ta amince da shirya irin wannan taro na ƙasa da ƙasa aƙalla sau biyu a shekara, domin baiwa kwalejin kimiyya da fasaha da sha’anin mulki zama cibiyar ilimi ta koyo da koyarwa.

Dakta Muttaƙa Rabe Darma ya bayyana cewa hukumar gudunmawar ta wannan kwaleji ta amince da kafa sashen koyar da ɗalibai sana’o’i domin dogaro da kan su bayan kammala wannan makaranta.

“Abinda muke fata shi ne, duk ɗalibin da ya kammala wannan kwaleji zai fita da aƙalla sana’o’i guda hudu da ya koya wanda za su taimaki rayuwarsa ya tsaya da ƙafarsa a cikin al’umma ” inji shi

Ya ƙara da cewa baban fatan da suke da shi a yanzu shi ne samar da ɗalibai da suke da tarbiyya a bangaren ilmin da dabi’a da za a riƙa girmamawa acikin al’umma sannan su yi gogayya a matakin ƙasa da kungiyoyi.

Haka kuma Dakta Muttaƙa Rabe Darma ya bada sanarwar kammala wa’adin aikin shugaban kwalejin kimiyya da fasaha da sha’anin mulki ta KSITM a ranar 12/12/2024 wanda ya ce tuni an aiyana wanda zata riƙe kwalejin kafin a samu cikakken shugaban da zai jagororinci kwalejin.

Ya ƙara da cewa daga zuwan su har sun amince da karin girma ga wasu Malamai 17 da ma’aikatan kwalejin guda 16 a wani mataki na dawo da martabar kwalejin a idon duniya tare da tsarawa kwalejin hanyar zata riƙa samar da kuɗaɗan shiga ba tare da ta yi kaziri-kaziri ba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *