September 17, 2026

Kwamishina Ya Gwangwaje EXCOn APC Da Naira Miliyan 3 Su Sha Ruwa A Katsina

0

Daga Wakilinmu

Kwamishina ma’aikatar tsare-tsare da tattalin arziki na jihar Katsina, kuma Jiga a Jam’iyyar Hon. Faruk Lawa Jobe ya taya sabbin shuwagabanin jam’iyyar APC na karamar hukumar Kankara da suka samu nasara a zaban da ya gabata tare da jika su da kudi naira miliyan uku domin watayawa.

Taron wanda ya gudana a sakatariyal karamar hukumar Kankara da  ke jihar Katsina na da nufin sada zumunci da kuma taya murna ga sabbin shugabannin Jam’iyyar APC da aka zaba tun daga matakin mazabu zuwa matakin karamar hukuma a cikin shekarar da ta gabata.

Tunda farko da yake jawabinsa yayin gudanar da taron Hon. Faruq Lawal Jobe ya gaisa da sabbin shugabannin jam’iyyar, tare da yi masu addu’ar fatan alheri, Allah ya tayasu riko, ya basu ikon yin adalci bisa tafiyar da shugabancin da Allah Ya dora masu.

Bayan kammala jawabinsa ne kwamihsina ya bada kudi wuri na gugar wuri har naira miliyan uku  ga shuwagabanin domin su yi wasu hidimomin yau da kullu a matsayin gudunmawarsa, na dan asalin karamar hukumar Kankara

Shima a nashi jawabin, babban bako a wurin taron Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina Alh. Bala Abubakar Musawa ya yaba tare da godema Kwamishinan akan kulawa da ya yi da shuwagabannin jam’iyyar APC sannan ya kira su taro domin sada zumunci da fatan alheri.

Bala Abu Musawa wanda ya yi kira ga shuwagabannin jam’iyyar APC da su tashi tsaye da addu’a da niyyar Allah ya yaye wadannan bala’o’i na rashin tsaro da ake fama da su, wanda ya shafi karamar hukumar Kankara.

Taron ya samu halartar mai baiwa gwamnan Jihar Katsina shawara akan harkokin siyasa Hon. Kabir Shu’aibu Charanci wanda ya samu wakilcin Darakta mai kula da harkar siyasa, Daraktan kudi da mulki na karamar hukumar Kankara, Mataimakin Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Katsina Alh. Umar Tsoho Mustapha. Dadai sauransu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *