A Shekara Ɗaya Ya Samar Da Hanyoyi Biyar A Ƙaramar Hukumar Katsina
A Shekara Ɗaya Ya Samar Da Hanyoyi Biyar A Ƙaramar Hukumar Katsina
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya Hon. Sani Aliyu Danlami ya sake kaddamar da aikin hanyar da ta tashi daga gidan Dawa zuwa Masallacin G.R.A.
Wannan dai ita ce hanyar ta biyar da ɗan majalisar ya ƙaddamar da fara aikin su, inda yanzu an kammala uku daga cikin biyar a shekara ɗaya da kotu ta tabbatar da nasa nasarar wannan kujera.
Wannan Hanya dai jama’a da dama sun bayyana cewa an yi ta lokacin da ake buƙatar ta, kuma zata taimaka matuƙa gaya ga al’ummomin wannan yanki na gidan Dawa
A tarihin ƙaramar hukumar Katsina wannan shine karo na farko da aka taɓa zuba ayyuka wanda wani ɗan majalisa ya samo daga gwamnatin tarayya tun bayan dawowa mulkin dimokuraɗiyyar a shekarar 1999.
Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamar da wannan gagarumin aikin hanya, Hon Sani Aliyu Ɗanlami ( Mai Raba Alheri) ya bayyana cewa idan aikin wannan hanya ya yi nisa akwai sauran guda huɗu na nan zuwa duk acikin ƙaramar hukumar Katsina.
Ya ƙara da cewa, ita wannan hanya da ya ƙaddamar da aikin yin ta, tana daga cikin alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yakin neman zaɓe saboda haka yana shaidawa al’umma ya sauke wannan nauyin.
A cewar sa, sauran hanyoyin da ke kan hanyar ƙaddamarwa sun haɗa da guda biyu da ke cikin unguwar Modoji da kuma kusa da ofishin hukumar hana fasa kwabri ta ƙasa (Customs) da kuma ƙarin wata a unguwar lay out.
Baya ga waɗannan hanyoyi da ya zuba a cikin garin Katsina akwai asibiti da ake cikin aikin ta a mazaɓar Shinkafi B sannan da ƙarin wasu ajujuwa guda shida a makarantar firamare ta Sani Aliyu Ɗanlami da ke unguwar Jan-Bango duk cikin birnin Katsina.
Ga jerin hanyoyin da Dan majalisar ya nemowa al’ummarsa domin inganta rayuwar su da kuma hanrkokinsu na yau da kullum;
1. Tashar Rabe – Janbango – Bypass tare da Hanyoyin Ruwa gefe da gefe
2. Hanyar Kofar Sauri Zuwa Lambun Danlawan zuwa Kukar Gesa Zuwa Kwarin Tama Zuwa Yandadi Ta bulle Bypass kuma da Hanyoyin Ruwa gefe da gafe.
3. Hassan Usman Road gefen Dutsinma Street – Kafur Road tare da Hanyoyin Ruwa gefe da gefe da kuma solar mai Amfani da Hasken Rana guda 24 a bisa Hanyar.
4. Bayan Sabon Gari Police Station ta biyo ta Yashe street ta tsallaka musawa street ta hade da kafur Road tare da Hanyoyin Ruwa gefe da gefe da kuma Fitilu masu Amfani da Hasken Rana guda 25
5. Bakori Road VIA Tambu street VIA Onoja Road Along musawa Street – Yashe Street tare da Hanyoyin Ruwa gefe da gefe da kuma Fitilu masu Amfani da Hasken Rana guda 40.
