Ban Mutu Ba ina Nan A Raye Cikin Koshin Lafiya inji Sanata Abu Ibrahim.
Ban Mutu Ba ina Nan A Raye Cikin Koshin Lafiya inji Sanata Abu Ibrahim.
Tsohon Sanatan Katsina ta kudu Sanata Abu Ibrahim ya ƙaryata jita -jitar da ake yadawa cewa Allah ya yi masa rasuwa inda ya ƙara da cewa yana nan cikin koshin lafiya
Labarin rasuwar Sanata Abu Ibrahim ya karade dandalin sada zumunta na zamani inda ake ta kai komo da batun mutuwar ta sa, sai dai babu inda aka bayyana cewa daga iyalansa aka samo labarin.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da aka yi da Sanata Abu Ibrahim ya bayyana cewa suna tare da direban sa a mota yake nuna masa labarin rasuwar sa a kafar sadarwa ta soshiyal midiya.
“Kasan ita yarda da mutuwa imani ne saboda haka har yanzu ina nan da raina kuma cikin koshin lafiya, muna jira hukuncin Allah ta’ala ” inji shi.
Acikin wata sanarwa da iyalansa suka fitar wanda kuma jaridar Daily Trust ta wallafa, iyalansa sun bayyana cewa wannan batu ba gaskiya ba, mahaifin su yana na raye cikin koshin lafiya.
Sanarwar wanda baban Ɗan Sanatan Alhaji Muhammad Abu Ibrahim ya sanyawa hannu ya karin haske da cewa labarin rasuwar mahaifin na su ta fara ne tsakiyar dare yau Lahadi 1 ga watan june, 2024.
Kazalika iyalan tsohon Sanata na kira ga al’umma da su yi watsi da wancan labarin da ke cewa Allah ya yi wa mahaifin su rasuwa, suka ce lokacin rasuwar ta sa bai yi, abu ne da ke hannun Allah ta’ala.
