Mai Raba Alheri Ya Raba Buhun Shinkafa 2,000 A Ƙaramar Hukumar Katsina
Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya Hon Sani Aliyu Ɗanlami ya buhunnan shinkafa da Gero da kuma Masara 2,000 ga jama’a daban-daban.
Wannan rabo na da nufin rage radadin da jama’a ke fama da shi na matsin tattalin arziki da al’umma ke fuskanta a Nijeriya baƙi ɗaya.

Da yake jawabi a wajen bikin bada wannan tallafi ɗan majalisar ya ce suna koyi da irin huɓɓasar da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ke yi na tallafawa marasa karfi musamman a wannan watan na Ramadan.
‘Kishi da tausayi irin na mai girma gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa yasa muma muka bi sahu wajan gani dacewar yin namu ƙoƙarin domin dai a tallafawa marasa karfi’ inji shi

Honarabul Sani Aliyu Ɗanlami Mai Raba Alheri ya yi bayanin cewa an kasa mutane kashi daban-daban ta yadda ɓangarori za su amfana da wannan tallafi ba tare da wasu sun yi korafi ba.
Yana mai cewa an zaɓi marasa galihu mutum 1,000 sai ku.a kungiyoyi mutum 500 a ya yin da shugabannin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya za su amfana da buhu 500.

A nasa, jawabin gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya nuna jin daɗin sa da wannan ƙoƙari na ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya Hon Sani Aliyu Ɗanlami ya yi na bada wannan tallafi
Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ce yanzu batun ciyarwa na daga cikin abubuwan da gwamnati tasa gaba ba, a cewar sa, za a ƙaddamar da raba tallafi a matakin kananan hukumomi 24 na jihar Katsina.

Haka kuma gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ganin ta samar da ayyukan yin bayan raba abinci ga al’umma domin sauƙaka masu rayuwa a wannan lokaci na watan Ramadan.
