September 19, 2026

Manyan Dalilan da Suka sa ‘ Yan Bindiga suka Zafafa Kai Hare-Haren Rashin Imani. Daga Yazid Nasudan 

0

Daga sati uku zuwa yanzu, na san kowa ya lura da yanda yan ta’addan daji su ka zafafa kai hare haren rashin Imani irin na kan mai uwa da wabi, tun daga garin zurmi a jihar Zamfara zuwa Danmusa kurfi da kankara a jihar katsina, da kwasar daliban firamare a kuriga jihar kaduna, da daukar almajirai a jihar Sokoto.

1. Duka wadannan hare haren su na da alaqa da abinda Bahaushe ke cewa “Shure shure baya hana mutuwa”. Tun da aka fara ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso yamma ba’a taba samun wani lokaci da yanta’addan ke fuskantar matsi da mummunar baraza ba irin ta wannan lokacin.

2. Bayan kaddamar jami’an CWC a jihar katsina kwarin guiwar al’uma ya karu matuka inda mutanen gari hade da jamian tsaro da yan CWC ke tunkarar barayin nan gaba da gaba a fafata ayi kare jini biri jini, wani lokaci ma ba a jiran su su kawo hari, bin su ake a Kai masu harin har inda su ke.

Su na Kai irin wadannan hare haren domin tsorata al’uma da dakile karsashi da kwarin guiwar da su ka samu na Kai masu hari ko tunkarar su Kai tsaye.

3. A cikin wadannan yan watannin an gano imfoma da yawa kuma an dauki mataki a kansu. Saboda haka yanzu kai hari yanda suke a baya na su je Kai tsaye su dauko mutum yana yi masu wuya.

Tunda samin bayanai ta hanyar imfoma ya yi masu wahala don haka sai su ka koma yin amfani da irin wannan hanyar ta shigowa gari su na harbin kan mai uwa da wabi, musamman domin daukar fansar imfoma din su da aka gano aka dauki mataki a kansu.

4. Bayan kirkiro CWC a jihar katsina, yunkurin sauran jihohin kaduna, Zamfara da Sokoto na samar da na su jami’ai ya na firgita yan ta’addan nan, musamman yanda su ke ganin al’uma na goyon bayan yunkurin tare da ganinsa a matsayin mafita.

Saboda rage wannan karsashin sai su ka zafafa wa al’uma hare hare, a ganinsu hakan zai Kara bakantawa gwamnonin rai, tare da nuna cewa duk yunkurin da suke yi a banza yake.

Mafita

1. Gwamnoni su cigaba da yunkurin da suka fara kada guyawunsu su sare, kada su gajiya, akwai alamun nasara kusa in sha Allahu.

2. Su Kara kokarin ganin hadin kansu da yin aiki tare da juna ya dore, domin kowace jiha ba zata iya samun nasara ba tare da hadin kan makwabciyar ta ba .

3. Su kara bude kofofin samun shawarwari da gudummuwa daga dukkan masu ruwa da tsaki a jihohin su, domin hannu daya baya daukar jinka.

4. Su bude asusun tallafawa al’umar da su ka tagayyara da wadanda su ke Kara tagayyara, musammnan wadanda su ka baro garuruwansu. Domin Rashin yin hakan zai iya samar da wata sabuwar matsalar bayan waccan.

5. A nemo wasu sabbin dabarun kula wa da karatun kananan yaran da su ke ragaita bisa titunan biranen mu wadanda da yawansu basa da wata makoma, wadannan yaran nan gaba za su iya zama kalubalen da yafi wanda ake ciki yanzu.

6. Kada al’uma su yanke kauna, komi yayi farko yana da karshe.

7. Kowa ne gari, kowane kauye su hada kai su ga irin dabarun da za su iya yi domin sama wa kansu mafita gwargwadon karfinsu.

Allah ya kawo mana zaman lafiya Mai dorewa.

©Yazid Nasudan
10/ March 2024

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *