September 18, 2026

APC Zata Sanya Kafar Wando Daya Da PDP Bisa Zargin Kaiwa mutanen Ta Hari A Zamfara

0

Daga Hussaini Ibrahim

Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta gargaɗi shugabannin jam’iyyar PDP a jihar da su daina kai wa ‘ya’yanta hari ko kuma su sanya kafar wando ɗaya da Jam’iyyar PDP.

Da yake jawabi ga manema labarai a Gusau a jiya Laraba, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris, ya ce, APC ba za ta ƙara lamunta da cin mutuncin ‘ya’yanta ba daga magoya bayan jam’iyyar PDP ke yi a yayin gudanar da harkokinta na siyasa ba.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Alhaji Yusuf Idris yayin taron manema labarai

Idris ya ce, yanzu jam’iyyar APC a shirye take ta ɗauki tsattsauran mataki a kan shugabannin PDP idan ba su daina ɓarnata kadarorinsu ko kuma muzgunawa mambobinta ba.

Ya ce, “Muna so mu yi gargaɗin cewa abin da ya faru a ranar Litinin da ta gabata yayin gangamin PDP ya zama karo na karshe da PDP ko wasu bata-gari da ke ɗaukar nauyinta za su yi mana da tashin hankali ko hali”.

Jam’iyyar APC muna da damar da za mu iya fuskantar su kowane lokaci, a ko’ina kuma za mu kasance a shirye don kare kanmu da mutumcin ‘yan APC.”

“A koyaushe muna goyon bayan gwamnati da hukumomin tsaro wajen wanzar da zaman lafiya, doka da oda a jihar kuma za mu ci gaba da bada goyan bayan a ko da yaushe”.

“Amma ba za mu amince da wani hari ko cin mutunci ko fasa Mana motoci da ke dauke da hotunnan jam’iyyar muba”

“A halin yanzu muna yakin neman zaɓe da kuma neman kuri’u daga masu zaɓe kuma su ma ya kamata su yi hakan ba da tare da tsakanar mu ba”.

“Mu a jam’iyyar APC da gwamnati ke kan mulki da kuma masu goyon bayan mutanen jihar, mun tsaya tsayin daka wajen ganin gwamna Matawalle ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar”.

Akan haka ne Yusuf Idris yayi kira da babbar murya ga shugabani PDP da su tsawata ma manbobinsu akan fida daga lamuran mu da kuma yi mana ta’annati ga duk wata ƙadara ta jam’iyyar APC idan ko ba haka ba jiki magayi inji Yusuf Idris Gusau.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *