An Yi Garkuwa Da Sabon DPO A Jihar Plateau.
An yi garkuwa da DPO na karamar hukumar Pankshin dake jihar Plateau kwanaki kadan da kama aikinshi a wurin.
Ba a dai samu mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Alfred Alabo ba don yin karin haske kan lamarin.
Sai dai wani mazaunin garin Pankshin da bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard cewa a ‘yan kwanakin nan ana yin garkuwa da mutane a yankin, yanzu haka ma kowa na cikin fargaba.
A cewarsa, “Lamarin ya faru ne a kusa da gidanmu, yayin da muka kammala sallar isha’i tare da iyalina, sai muka ji karar harbe-harbe, muka yi kokarin jin abin da ke faruwa, sai muka samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga suka je otal din Woktori. Da safiyar yau ne muka samu labarin cewa masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da sabon DPO na Pankshin. Mun samu labarin cewa mutumin ya kwana ne a otel suka zo su sace shi.”
“Kowa na cikin fargaba saboda ko da daren nan tsakanin karfe 7 zuwa 8 na dare, an yi ta jin ƙarar harbe-harben bindiga, amma ba mu san ko ina bane ba. Abun ya zama ruwan dare, harma an saba da shi. Zuwa gobe za mu ji meye musabbabin hakan. DPO ɗin dai sabo ne, ba mu san shi ba saboda bai dade da kama aiki ba aiki.”
