Matar Gwamnan Zamfara Ta Ƙaddamar Da Bada Tallafin N50,000 Ga Mata Dubu Huɗu A Gusau
Daga Hussaini Yero
Uwargidan gwamnan jihar Zamfara,Hajiya Huriya Dauda ta ƙaddamar da bada tallafin naira dubu hamsin ga Mata dubu hudu dan dogara da kai wajan harkar sana’ar su.
Hajiya Huriya Dauda ta ƙaddamar da tallafin ne yau a Gusau’ babban birnin jihar Zamfara.
A wajabin ta, Huriya Dauda ta bayyana cewa,kamar yadda kuka sani, wannan gwamnati babban Kudirin ta shine taimakon rayuwar mutane, musamman ma marasa galihu. akwai bukatar karfafawa da tallafawa mata, kuma mata sama da dubu hudu a fadin jihar za su ci gajiyar wannan tallafin na naira dubu hamsin.inji Huriya Dauda”.
“Munyi haka ne don ganin iyayenmu mata su zama masu dogaro da kansu, tare da lura da kalubalen da ake fuskanta sakamakon tabarbarewar tattalin arziki”.
“Wannan shirin karfafawa na sana’a ya yi nisa ne domin tallafawa mata dubu hudu a fadin jihar da naira dubu hamsin domin rage radadin wahala da kuncin rayuwa da ake ciki.
Ina roƙon ku da ku yi amfani da kuɗin wajan yin qananan kasuwancin da kuka zaɓa ko kuma wace kukeyi ayanzu a gidajanku.
Daya daga cikin wadanda suka amfani da tallafin,Fatima Ibrahim ta bayyana godiyar ta ga ga Allah da kuma addu’a ga gwamnatin jihar Zamfara karkashin Jagorancin gwamna Dauda Lawal na cimma kudirinsa na cigaban jihar Zamfara baki daya.
