September 18, 2026

Magidanta 168,000 Ne Zasu Amfana Da Tallafin Abinci Daga Sanata Yari A Zamfara

0

Daga Hussaini Ibrahim

Magidanta 168,000 ne zasu amfana da rabon tallafin Abinci daga Sanatan Zamfara ta Yamma,Dr Abudulaziz Yari Abubakar domin ya rage masu radadin mawuyacin halin da ake ciki.

Shugaban kwamintin yada labarai na bada tallafin, Hon Ibrahim Birnin Magaji ne ya bayyana haka a takardar da ya sanya mahannu ga manema labai a Gusau.

Acewar sa,Jagoran tafiyar Siyasar Sanata Yari,Hon Lawali Liman Kaura ne ya kaddamar da kwamitocin raban kayan tallafin dan ganin an bada tallafin yadda ya kamata fadin jihar ta Zamfara.

Kuma mutane kananan hukumomi goma sha hudu ne zasu amfana da wannan tallafin a fadin jihar ta Zamfara.

Daga cikin wadanda zasu amfana da tallafin sun hada da marayu,gajiyayu ,’yan gudun hijira da masu bukata ta musamman da dai sauran su.

Kuma dau’in Abinci da za’a raba sun hada Shinkafa,Masara,Gero da Sauran su.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *