Tinubu Zai Yiwa Yan Nijeriya Jawabi A Daren Yau.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasar da karfe 7 na dare a yau Litinin, 31 ga Yuli, 2023.
Dele Alake, mai magana da yawun shugaban kasar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Litinin.
Sanarwar ta kara da cewa, “gidajen talabijin, gidajen rediyo da sauran kafafen yada labarai zasu jona gidan talabijin na Najeriya da Rediyon Najeriya don watsa shirye-shiryen,” in ji sanarwar.
Ba a dai san ko me za a yi bayani ba, amma ya zo ne a daidai lokacin da mutane ke korafin halin kuncin da kasar ke ciki sakamakon cire tallafin mai, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta bayyana.
