Tsaro: Ƙaramar Hukumar Ɗandume An gabatar da Addu’a Samun Zaman Lafiya
Daga Hussaini Yero
Matsalar tsaro da ta addabi al’ummar Karamar hukumar Dandume A yau Talata,manyan malamai da Alaramomi sun gabatar da saukar Alkur’ani da addu’oi na musamman dan samu dawamamem zaman lafiya, a Karamar hukumar da Jihar Katsina da Kasa baki daya.
Shugaban Karamar hukumar Dandume ,Hon Basiru Musa ne ya ga batar da Jawabin kafin Fara addu’oin inda ya bayyyana cewa,babu babban garkuwar mu a yau wace ta wuce addu’a dan addau’a itace jigon kariya ta alummar.inji Shugaban Karamar hukumar.
“Hon Bashir Musa ya kara da cewa, Mahara sunyi nifi gamawa da mutanan karamar hukumar amma zuwa yanzu daukar mumuke sukeyi ,Sakamakon adduoi da mukeyi ne Allah ke bamu kari akan su dan mugunnifin su su tarwatsa al’ummar Karamar hukumar Amma ta Allah ba tasu ba.
Wannan adduar kuyi ne ga Gwamna Diko Rada ga duk abunda zai aiwatar sai ya gabatar da addu’a akoda yaushe aduaar sa itace abunda ba alhairiba ne a gare shi da al’umma kada Allah ya bashi shi.dan haka mu ke koyi da Mai daraja gwamna Rada wajan saya addau’a gaban komai.
Jagora gabatar da addu’a shine Malam Barhamu Shek Abdullah ya bayyyana cewa,addua a wajan su Koda yaushe ne su keyin ta amma wannan ta musamman ce ,wace muke gabatar da ita duk daya ga watan ogusta a cikin gangami dan samun tabarakin juna akan Allah ya magance mana matsalar tsaro da ta addabi mu da Jihar Katsina da Kasa baki daya.
Ansa jawabin Katukan Katsina Hakimin Dandume da ya samu wakilcin ,Shamsu Ibrahim Magajin Jiruwa,yayi kira ne ga gwamnati da ta taimaka wajan samarwa alumma saukin rayuwa dan yanzu haka muna cikin mawuyacin hali.na tsadar rayuwa da rashin tsaro.
