September 18, 2026

Sarkin Katsina Ya Kaddamar Da Cibiyar Kiwon Lafiya Da Makaranta A Katsina.

0

Sarkin Katsina ya kaddamar da cibiyar kiwon lafiya ta al’umma mai suna Hambali Family Comprehensive Community Health Center da makarantar Islamiyya da raunon yara mai suna Muhammadu Shumo Islamiyya and Nursery Schools a Unguwar Alkali, cikin garin Katsina.

Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman ya yaba ma kungiyar iyalin Hambali bisa yin ayyukan.

Sarkin ya bukaci sauran masu wadata da ke cikin al’umma su kwaikwayi irin haka domin ci gaban yankunansu.

A tsokacinshi, shugaban kungiyar iyalin Hambali Justice Umar Abdullahi ya ce iyalan sun yanke shawarar gina cibiyar kiwon lafiyar da Islamiyyar ne domin bunƙasa ilimi da kiwon lafiyar iyalansu.

Justice Umar Abdullahi ya gode ma sarkin Katsina bisa bada tabbacinshi na samar da makaranta da teburra da kujeru tare da gyara dandamalin makarantar.

Tunda farko a jawabinshi, babban shugaban kungiyar Misbahu Na-Iya ya gode ma masu ruwa da tsaki da suka bada gudummawa aka kammala ayyukan.

Misbahu Na-Iya ya roƙi membobin kungiyar su bada gudummawa da zata taimaka ma ɗorewar ayyukan.

Kaigaman Katsina Kabir Muhammad Mashi ya ce sarkin Katsina ya zama matsayin uba da ɗan-uwa ga iyalan Hambali.

Kabir Mashi ya kuma gode ma ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Katsina a majalisar dokokin jihar Katsina Ali Abu Albaba bisa bada gudunmawar naira N300,000 ga cibiyar.

Sauran mutanen da suka halarci wurin sun haɗa da Jafaru Yusuf Riyojin Katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *