Layin Man Fetur Ya Sake Dawowa A Abuja Kan Karin Farashin Man Fetur.
Layukan man fetur sun sake kunno kai a Abuja, babban birnin Najeriya, sakamakon karin farashin man fetur.
Majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa, an sake ƙara farashin man fetur ɗin da ake sayar da shi Naira 537 kan kowace lita a babban birnin kasar a daren jiya zuwa N617 a wasu sassan Abuja a safiyar ranar Talata.
Saidai hakan ya haifar da rububin sayen man, yayin da masu ababen hawa ke tururuwar zuwa sayen man a gidajen mai da ke birnin.
A gidan man AA Rano da ke Utako, cike ya ke da ababen hawa ciki da waje.
Wakilin jaridar Dailytrust da ziyarci gidajen mai da dama a tsakiyar birnin inda ake bin layukan har zuwa kan titi, ya ce yana jawo cunkoson ababen hawa.
