November 17, 2026

An Harɓe Mai Adaidaita Sahu A jihar Imo.

0

Masu aiwatar da dokar zama a gida ba bisa ka’ida ba na kwanaki bakwai sun sake harbe wani mai adaidaita sahu da mai tafiya a ƙasa har lahira a mahadar Akwakuma da ke karamar hukumar Owerri ta Arewa a jihar Imo.

‘Yan bindigar, kamar yadda rahotanni suka bayyana, sun yi hakan ne a ranar Asabar a yayin da suke aiwatar da dokar zama a gida, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta Leadership ta bayyana.

Wani ganau ya ce ‘yan bindigar sun afka wa yankin ne a cikin wata motar safa ta Sienna, inda suka fara harbe-harbe kan iska, lamarin da ya sa mutane suka yi ta gudun tsira da rayukansu.

Mai adaidai sahun wanda har yanzu ba a gano sunansa ba, an ce yana lekowa fasinjojin mahadar, yayinda ‘yan bindigar suka harbe shi a kirji.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da aka kona wani bangare na kasuwar Orie Amaraku tare da wasu motoci da aka aje, wanda ake zargin jami’an tilasta bin dokar zama a gidan ne suka yi hakan.

Wata tela da ke mahadar Akwakuma, wadda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar LEADERSHIP cewa, an harbi wani mai tafiya a kasa a lokacin da suka kai harin.

A cewar ta, “Abin takaici, a halin yanzu mahadar ba kowa saboda ‘yan bindigar. Sun harbi mai adaidaita sahu daya da wani mai tafiya a kasa.

“Ina cikin shago na aka fara harbe-harbe akan iska duk muka gudu. Ko da yake ban ga ‘yan bindigar ba, amma na ji karar harbe-harbensu sosai.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Henry Okoye, bai ce komai ba akan lamarin ba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *