November 18, 2026

ACF, JNI, CAN Sun Yi Allah-Wadai Da Kashe-Kashen Jihar Plateau.

0

Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF), Jama’atu Nasril Islam (JNI) da kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) sun yi Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato da wasu sassan jihar Benue.

Wannan na zuwa ne yayin da wasu ‘yan bindiga suka kashe akalla mutane takwas ciki har da jariri dan watanni takwas a unguwar Farin Lamba da ke gundumar Vwang ta karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato a daren Lahadi.

Lamarin ya zo ne kwana guda bayan wani hari da aka kai a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Mangu ta jihar inda aka ce an yi asarar rayuka da dama tare da kona gidaje.

Majiyar Popular News Hausa ta jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa, kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) a ranar Lahadin da ta gabata ta bayyana cewa an kashe mambobinta 15 a farmakin da aka kai musu.

Kungiyar ta kuma ce an kona gidaje 78 na mambobinta, yayin da sama da shanu 2,000 suka bace bayan harin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Alabo Alfred, bai amsa kira da sako da wakilin majiyar Popular News Hausa ya yi masa kan sabon harin da aka kai lokacin hada wannan rahoto ba.

Sai dai sakataren yada labaran kungiyar Berom Youth Mooulders, Rwang Tengwong, ya ce maharan sun isa unguwar ne da misalin karfe 9:45 na dare lokacin da mutanen ke barci.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *