November 17, 2026

Manoman Ondo Sun Kai Ɗan Akeredolu Kotu Kan Lalata Shukar Koko.

0

Wata babbar kotun jihar Ondo da ke zamanta a Ondo, hedikwatar karamar hukumar Ondo ta Yamma a jihar, za ta saurari wata ƙara akan Babajide Akeredolu, dan gwamna Rotimi Akeredolu, inda ake kalubalantar lalata gonakin koko a dajin Oluwa a karamar hukumar Odigbo ta jihar.

Da yake shigar da Babajide ƙara akan lamarin, lauyan manoman, Tope Temokun, ya faɗa ma kotun cewa yana da muhimmanci a saka Babajide cikin shara’ar saboda ana zargin ya bada umarnin share gonakin na koko a matsayin shugaban sashen sanya ido na bangaren aiwatar da ayyuka a jihar Ondo (PPIMU).

Ya shaida wa kotun cewa hekta da dama na gonakin Cocoa mallakar manoman ne ake zargin kamfanin SAO Agro-Allied Services Limited ta lalata.

Da yake gabatar da kansa, Dokta Abudul-Kabir Ajana ya ce ya tsaya a madadin dukkan waɗanda ake kara a shari’ar da suka hada da Fasto Akin Olotu, babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin noma wanda shi ne ƙara na biyar.

Ya shaida wa kotun cewa yana da takardar neman yin watsi da hukuncin da kotu ta bayar a ranar 2 ga Mayu, 2023.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *