September 18, 2026

Tinubu Ya Bada Tabbacin Samar Da Kayan Rage Raɗaɗin Cire Tallafin Man Fetur.

0

Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba a Abuja, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, ana kan aiwatar da tsarin da zai taimaka wajen magance radadin cire tallafin man fetur, yana mai tabbatar da cewa matakin na da amfani ga kasar nan, musamman wajen tabbatar da ci gaba a nan gaba.

Shugaba Tinubu, wanda ya tarbi tsaffin gwamnoni 18 da suka yi shugabanci tare da shi a shekarar 1999 a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri, yayin da gwamnati za ta kara kokari don tabbatar da ganin an samu ci gaba, musamman wajen tura kuɗi a zamance, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership ta bayyana.

“Na fahimci cewa babu daɗin da za a sami ba tare da an sha wahala ba. Kuma bayan wuya sai dadi. An sake ruɗa Najeriya da cire tallafin mai. Hakan amfanin ɗunbin mutane ne, madadin wasu yan fasa-kwabri su riƙa amfana.

“Don Allah a gaya wa mutane su yi haƙuri.

A bangaren tsaro kuwa, shugaban kasar wanda tun da farko ya gana da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno domin duba halin da ake ciki a yankin Arewa maso Gabas, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya musamman jihar Filato da su maida hankali yin amfani da tattaunawa domin magance rikice-rikice,

“Za mu yi duk mai yiwuwa don daidaita kasar,” in ji shi.

Tsofaffin gwamnonin sun bukaci shugaban kasar da ya ci gaba da kudurin ganin Najeriya ta samu ci gaba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *