September 19, 2026

Kanwan Katsina Ya Taya Sabbin Shugabannin NUJ Reshen Jihar Katsina Murna.

0

Kanwan Katsina hakimin Ketare Usman Bello Kankara ya taya sabbin kaddamammun shugabannin kungiyar yan jaridar Najeriya rshen jihar Katsina dana kungiyar yan jarida mata ta Najeriya reshen jihar Katsina murna.

Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka aike ma shugaban kungiyar reshen jihar Katsina Tukur Hassan Dan Ali da shugabar kungiyar yan jaridar mata reshen jihar Katsina Hannatu Mohammed.

Kanwan Katsinan wanda shi ne uban kungiyar yan jaridar reshen gidan talabijin na jihar Katsina KTTV ya yi nuni da cewa, sake kaddamar da shugabannin kungiyar na tsawon shekaru 3 wata manuniya ce ta ci gaba karara, jajarcewa, rashin son kai da kuma tabbacin da yan jaridar ke da shi akan su.

Usman Bello Kankara ya yaba ma kungiyar yan jaridan bisa gina wurin wasa ga yan jaridar dake aiki a jihar, gyara sakatariyar su da sauran ayyukan a-zo a-gani dake da nufin bunkasa ayyukan yan jarida.

Basaraken ya bukaci su ci gaba da aiki yadda yakamata, da amfani da filin dake cikin sakatariyar don gina wuraren samun kuɗi da tara kudin shiga.

Kanwan Katsinan wanda shi ne uban kungiyar a ranar bikin kaddamar da shugaban ya yi kira ga yan jaridar dake aiki su riƙa daidai labarin su a koda-yaushe don guje ma yaɗa labarai ƙanzon kurege masamman ma a wannan lokacin na kafafen sada zumuntar zamani.

Taron dai ya samu halarcin matan zaɓaɓɓen gwamnan jihar Katsina Zulaihat Dikko Radda a matsayin babbar bakuwa ta masamman.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *