Majalisar Dattawa Ta Umurci Yan Sanda Su Binciki Ɓacewar Mukaddashin Kwamandan Hukumar Civil Defence.
Majalisar dattijai ta bukaci babban sufeton ‘yan sanda Alkali Baba ya binciki bacewar mukaddashin kwamandan hukumar tsaron Civil Defence Raymond Gaadi.
Shi dai Gaadi ya isa jihar ne domin kama aiki a hedkwatar hukumar tsaron Civil Defence ɗin dake jihar Bayelsa, amma da zuwansa yayi ɓatan dabo.
Majiyar Popular News Hausa ta Leadership ta bada rohon cewa hukumar tsaron Civil Defence ba ta nuna damuwa ba ko kadan ba kan lamarin tun bayan faruwar lamarin a ranar 29 ga watan Oktoba, 2022.
Matakin majalisar ya biyo bayan kudirin da Sanata Emmanuel Orker Jev ya gabatar na nuna rashin jin dadinsa kan bacewar Raymond Gaadi, mukaddashin kwamandan da aka tura daga Enugu zuwa jihar ta Bayelsa domin ci gaba da aiki, amma ba a ƙara jin duriyarsa ba.
Dan majalisar ya ce, mukaddashin kwamandan ya ankarar cewa jami’in da zai amshi aiki hannunshi nayi mashi barazana, baya ga nuna mashi turjiya ga kujerar da zai amsa.
Ya kara da cewa kwanaki biyu bayan da mukaddashin kwamandan ya yi kararsa kan barazanar da ake yi masa, sai yayi ɓatan dabo.
Sanata Jev ya koka da cewa hukumar Civil Defense ba ta nuna damuwa kan lamarin ba tun daga ranar 29 ga Oktoba, 2022.
Majalisar dattawan dai ta bukaci kwamandan Civil Defense ya jagoranci gudanar da binciken cikin gida kan lamarin.
Har ila yau kuma, ta bukaci babban sufeton yan sanda ya jagoranci gudanar da cikakken bincike akan bacewar Raymond Gaadi, mukaddashin kwamandan hukumar tsaron ta Najeriya.
