September 18, 2026

‘Yan Bindiga Na Neman Miliyan 10 A Hannun Iyalan Alhaji Zilkifilu Kafin Su Sako Shi.

0

Sakamakon harin da yan bindiga suka kai a Babar Ruga da ke cikin ƙaramar hukumar Ɓatagarawa inda suka kashe mutane biyu sannan suka yi garkuwa da ɗan kasuwa Alhaji Zilkifilu Sani sun magantu.

Majiyar Popular News Hausa daga ɓangaren iyalansa ta tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun nemi kuɗi har Naira miliyan goma a matsayin kuɗin fansa

Sai dai kuma iyalan nasa ba su yi ƙarin haske ba akan yiwuwar samar da kudin ko a a, amma dai Alhaji Zilkifilu Sani na cigaba da zama a hannun ‘yan bindigar har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Idan za a iya tunawa Alhaji Zilkifilu Sani yana ɗaya daga cikin mutanen da iftila’in gobara ya shafa a lokacin da Babar kasuwar Katsina ta kama da wuta.

Yanzu dai addu’ar da kowa ke yi ita Allah ya gafartawa mutanen da aka kashe ya kwato Alh Zilkifilu da Sauran mutanen da ke hannu,n yan ta’ada.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *