Boko Haram: Har Yanzu Ba A Maida Mutane 200,000 Matsugunansu Ba – Zulum.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa sama da mutane 200,000 da suka rasa muhallansu a yankin Arewa maso Gabas sakamakon rikicin Boko Haram har yanzu ba a maida da su gida ba.
Sama da mutane 200,000 sun kasance ‘yan gudun hijira a wasu kasashe makwabta, inda suka tsere domin ceton rayukansu daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram da suka addabi yankin.
Da yake magana a lokacin da yake gabatar da rahoton kungiyar Technical Working Group ga mataimakin shugaban kasa a fadar shugaban Najeriya dake Abuja, Zulum ya ce a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kimanin mutane 50,000 ne suka koma gida.
Gwamnan ya kuma yi kira ga mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda shi ne shugaban kwamitin shugaban kasa kan maido da ‘yan gudun hijira a shiyyar Arewa maso gabas da ya yi abinda ya kamata ta hanyar tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da izini cikin gaggawa ta fuskar kudade da kuma sake tsugunar da ‘yan gudun hijira, tare da sauran kayan aikin da ake bukata domin sake gina al’ummomin da aka lalata ma gidaje a jihar ta Borno.
Da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin jihar a karshen taron, Zulum ya ce, “shugaban kasa ya kaddamar da wani kwamiti a watannin baya da zai duba batun dawo da ‘yan asalin jihar Borno da sauran jihohin Arewa maso Gabas dake zaune a jamhuriyar Chadi, Kamaru da Nijar.
Ya ce “Mun gabatar da rahoton ga mataimakin shugaban kasar da nufin tabbatar da cewa, za a ci gaba da aikin dawo da ‘yan gudun hijira daga Kamaru nan take, yayin da za a dawo da dawo da ‘yan Najeriya mazauna Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Chadi nan ba da jimawa ba.”
Da aka tambaye shi kan adadin mutanen da aka mayar da su gidajensu, gwamnan jihar Borno ya ce, “A cikin ’yan shekarun da suka gabata, ba mu maido da mutane kasa da 50,000 ba, amma har yanzu muna da sama da 200,000.
Ya ce “Don haka abin da muke nema a yanzu shi ne mu ga yadda za mu dawo da ‘yan asalin Jihar Borno dake zaune a Nijar musamman wadanda suka fito daga kananan hukumomin Malumfatori da Abadam.
Zulum ya bayyana cewa, muna da ‘yan karamar hukumar Gwoza, karamar hukumar Bama, da suke san dawowa gida.
“Muna da ‘yan asalin kananan hukumomin Kukawa da Marte da ke zaune a kasar Chadi.
Don haka ya ce, “ina ganin mataimakin shugaban kasa zai yi abinda ya kamata don ganin cewa shugaban kasa ya ba da izinin fitar da kudade da sauran kayan aikin da ake bukata don sake gina wadannan al’ummomi a jihar Borno.”
Da aka tambaye shi halin da ake ciki na tsaro a jihar, gwamnan ya ce, “al’amarin tsaro ya inganta sosai inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership.
Idan ba a manta ba a watan Fabrairu ne shugaba Buhari ya kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan dawo ‘yan gudun hijira a shiyyar Arewa maso Gabas, inda ya nada mataimakinshi a matsayin shugaba.
