September 18, 2026

Ranar Litinin 09 Ga Watan Janairun 2023 Za A Koma Makarantum Firamare A Jihar Katsina.

0

Idan Allah ya kai mu ranar Litinin 09 ga wannan watan na Janairu za a koma makarantu a fadin jihar Katsina domin ci gaba da zangon karatu na 2.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar bada ilimin bai ɗayan Aminu Badaru Jikamshi.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, dukkan makarantun dake faɗin jihar Katsina zasu bude a ranar da aka sanya cikin sanarwar.

Sanarwar ta kuma yi kira ga iyaye su ci gaba da taimaka ma kokarin gwamnati domin ganin yaransu sun koma makaranta don ci gaba da karatu.

Ta ci gaba da cewa, hukumar za ta ci gaba da sanya ido akan umarnin komawa makarantar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *