November 17, 2026

An Ba Ƴan Kwana-Kwana Kashi, Tare Da Farfasa Masu Gilassan Mota Saboda Zuwa Makare A Anambra.

0

Wasu fusatattun mutane a wannan Lahadin sun fatattaki jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Anambra bisa zargin sun isa wurin da wata gobara ta tashi a makare.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban hukumar kashe gobara na Anambra, Mr. Martin Agbili, kuma aka rabawa manema labarai a Onitsha a ranar Litinin 2 ga watan shekarar 2023 Litinin.

Agbili ya ce lamarin ya faru ne a hanyar Atani, da ke kusa da Uga Junction, Onitsha, da misalin karfe 6 na yamma.

Ya ce mutanen sun farfasa gilassai da maduban motar kashe gobarar, tare da jikkata wasu daga cikin jami’an hukumar.

Shugaban hukumar kashe gobarar ya bayyana lamarin da aka yi cikin sabuwar shekarar a matsayin na dabbancin, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard

Kamar yadda ya bayyana, a ranar Lahadi ne 1 ga watan Janairu, 2023 da misalin karfe 06:00 na yamma, hukumar kashe gobara ta jihar Anambra, ta samu kiran tashin gobara a mahadar Uga ta hanyar Atani.

“Nan da nan, aka tura motar mu da jami’an kashe gobara zuwa wurin. Da isa wurin, sai ƴan isa suka far mana.”

“Sun jefi mu da duwatsu da sanduna da kuma karafa. Abin takaici, sun farfasa gilashin motocinmu na kashe gobara, tare da raunata wasu daga cikin ma’aikatanmu.”

” A daidai lokacin da suka fara jifar motarmu ta kashe gobarar ga kuma wuta nata ci, sai muka ji suna cewa, ‘yanzu ma kuka zo kashe wutar kenan?

“Mun yi ƙoƙarin tserewa ma mutanen dake fatattakarmu da motar mai fasashshen, haɗi da ma’aikatanmu da suka jikkata.”

“Wannan kyautar sabuwar shekara abin takaici ne matuka, yadda ma’aikatan kashe gobara na jihar Anambra za su yi maraba da sabuwar shekara da wannan ta’asar.

“Ba shakka za a gurfanar da wadanda suka aikata wannan mugun aiki gaban kuliya manta sabo, ” in ji Agbali.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *