September 18, 2026

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Amince Da Ɗaukar Ma’aikata 2,000 Na Rundunar Yaki Da ‘Yan Daba.

0

Daga Hussaini Ibrahim

Gwamnatin jihar Zamfara, ƙarƙashin jagorancin gwamna Bello Matawalle ta bada umarnin ɗaukar ma’aikatan 2,000 na rundunar yaki da ‘yan daba da shaye-shayen miyagun Kwayoyi.

Shugaban hukumar yaki da’yan daba na jihar Bello Bakyasuwa ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke bayyana nasarorin da hukumar ta samu na tsaftace tarurukan yakin neman zaɓe da yanzu haka ya ke gudana a Zamfara.

AJawabinsa , Bakyasuwa ya bayyana cewa, gwamna Bello Matawalle ne ya kafa hukumar a ƙarƙashin dokar zartarwa ta 2 domin yaki da ‘yan daba, shaye-shayen miyagun kwayoyi, da manyan laifuka.

‘ Yanzu haka mutane 6,700 ne suka karbi takardar neman aikin da suka haɗa da maza da mata, kuma ana ci gaba da tantance su.

“Wannan wani ɓangare ne na kudirin gwamnatin jihar na faɗaɗa ayyukan yaki da ‘yan daba, shaye-shayen miyagun kwayoyi, da sauran laifuffukan da ke da alaƙa da su a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar”.

“Da mun gama tantance ma’aikatan, za mu tura zuwa ƙananan hukumominsu, domin cugaba da yaki da waɗannan ɗabi’un” in ji Bakyasuwa.

Shugaban ya jaddada himmar hukumar na kawar da ‘yan daba, shaye-shayen miyagun kwayoyi, da sauran laifuka masu alaƙa.

Daga nan ya kuma gargaɗi jam’iyyun siyasa da su guji ɗaukar nauyin matasa a harkar ‘yan daba, shaye-shayen miyagun kwayoyi, da sauran laifuffuka masu alaƙa da su a jihar.

A cewarsa, hukumar ba zai bari kowa ya tada tarzoma a jihar da sunan siyasa ba.

“Kamar yadda nake faɗa a kodayaushe gwamnatin jihar ce ta kafa hukumar, ba don siyasa ba sai don inganta harkar tsaro da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

“ Bakyasuwa ya ƙara da cewa, an umurce mu da mu taimaka wa ƙoƙarin gwamnati da jami’an tsaro wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da jihar ke fuskanta

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *