September 19, 2026

Gwamna Masari ya ƙaddamar da aza harsashin ginin Ɗakin kwana da masallaci a cibiyar koyar da aikin kanikanci na zamani ta jihar Katsina.

0

Aiki aza harsashin ginin da aka kaddamar a yau Talata 27/12/2022 a harabar makarantar kimiya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina (HUK POLY).

Da yake bayani a wurin taron Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yaba da kokarin Shugaban hukumar ta kula kera motoci ta kasa Jelani Aliyu na kirkiro cibiyoyin gyaran motoci na zamani a fadin kasar da ya hada da Katsina.

Gwamnan ya cigaba da cewa” mu sani zamani na canza abubuwa da yawa a rayuwarmu kuma dole mu bi zamani in munason samun cigaba”.

Daga karshe, Masari yace wannan dalili yasa muka ga ya dace mu gina dakin kwanan Daliban da Masallaci ga wadadda zasu samu wannan horon. Domin saukaka ma dalibai Musamman wadadda suka fito daga kananan hukumomin dake fadin jihar.

Tun farko da yake jawabin Shugaban hukumar kulada kera Motoci ta kasa, Jelani Aliyu wanda ya samu wakilcin babban daraktan hukumar Abubakar Gumi yace” an samar da wannan Cibiyar ne dan inganta aikin kire-kire da kuma kawo Fasahar gyara ta zamani a jihar ta Katsina.

A jawabin sa na godiya, Shugaban Kungiyar kanikawa ta jihar Katsina, Alhaji Abbati ya nuna farin cikin sa da wannan kokari na bunkasawa da Zamanantar da Sana’arsu.

Alhaji. Abbati ya kara da cewa” Kungiyar su ta hada da kanikawan Motoci, na Mashina da kuma masu fenti, kuma sun hada kansu domin ciyar da wannan sana’o’i nasu.

Daga cikin wadadda suka tofa Albarkacin bakin su akwai Kwamishinan kimiya da fasaha Hon. Mustapha Muhammad kanti Bello Wanda ya samu wakilcin Babban sakaren ma’aikatar Hon. Mannir Talba Mashi

Mai baiwa Gwamna Shawara kan ilimi mai zurfi, Dakta. Bashir Usman Ruwan godiya da Shugaban Makarantar Kimiya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina, Dakta. Mudi Kurfi.

Taron ya samu halartar Shugabanni da Sakatarorin Kungiyar kanikawa na kananan hukumomin jihar Katsina, Shugabannin Kungiyar masu Fenti da sauran Al’umma jihar Katsina.

Katsina Beat

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *