NUJ ZamfaraTa Ƙaddamar Da Kwamitin Ɗa’a Da Ladabtawa
Daga Hussaini Ibrahim.
Kungiyar ‘Yanjaridu rseshen Jihar Zamfara watau ( NUJ ) ta kaddamar da kwamitin da’a da ladabtarwa mai mambobi tara a yayin taron ta a jihar.
A cewar shugaban NUJ na Zamfara Kwamaret Ibrahim Musa Maizare, ya ce aikin jarida na taka muhimmiyar rawa wajen tsarkake harkokin siyasa da hanyoyin tafiyar da ayyukan gwamnati.
“Abin takaici ne ganin yadda a yanzu ana tauye ka’idojin aikin jarida, wanda hakan barazana ce ga martabar aikin”.
Waɗanda aka zaɓa a matsayin kwamitin da’a da ladabtarwa sun haɗa da Muhammad Tanko Khalil a matsayin shugaba da Haliru MB Umar a matsayin sakatare.
Sauran sun haɗa da Ibrahim Garba Tunau da Usman Muhammad Maru da Ibrahim Muhammad Kanoma da Kefas Habila Dogon Yaro da Bashir Sanda da Aliyu Adamu da Aisha Abdullahi Ja’o sune mambobin Kwamitin..
Kwamaret mai zare ya bayyana cewa a ƙoƙarin da ake na magance wannan matsala ta taɓarɓarewar tarbiyar aikin jarida wannan kwamitin zai taimaka gaya wajan tsaftace aikin jarida a jihar inji shugaban.
“Kungiyar ta NUJ a yau tana kaddamar da kwamitin da’a dan zabo tsofaffin ‘Yan jarida da suka yi aiki kuma suka bar tarihi a wannan jiha don su zama membobin kwamitin.”
“ Matakin ya yi daidai da sashi na 7 na kundin tsarin mulkin NUJ wanda ya umurci Kungiyoyin jihohi su kafa irin wannan kwamiti.
“Ina so in yi amfani da wannan damar don yin kira ga abokan aiki na da su bai wa kwamitin hadin kai wajan samun nasara aikin su kuma ba anyi kwamitin bane dan cin zarafin wani munyi shine dan taimakon kan mu da kanmu..”
Da ya koma kan nasarorin da suka samu ya bayyana cewa, a cikin watanni hudu da aka zabe su sun samu nasarar gyaran motocin kungiyar da ofisoshi a cibiyar ‘yan jarida.
“Mun kuma sami damar ci gaba da kyautata dangantaka tsakanin ‘yan jarida masu aiki a cikin Jihar.”
“Ina so in yaba da irin kulawar da kafafen yada labarai ke da shi daga gwamnatin jihar Zamfara.
Shugaban NUJ na jihar ya yabawa gwamnatin jihar bisa kafa gidan FM na Gols City da kuma gyara gidan rediyon Zamfara a jihar.
“Muna fatan za a mika wannan karimcin ga gidan jaridar jihar, gidan jaridu daya tilo a jihar.”
Tshohon kwamishinan yada labarai Hon Ibrahim Birnin Magaji ,da Sakataren Kungiyar NUJ na shiyar Arewa ma Arewa , Kwamaret Abdurazak kaura ne suka gabatar da kasidu akan kyautata da’ar aikin jaida ga ‘Yan Jaridu.
Shima anasa jawabin shugaban tsangar koyan aikin Jarida na kwalejin kimiya da fasaha ta gwamantin Jihar da ke Gusau watau (ZACAS) Malam Muhammad Tukur Janyau ,ya yaba da kokarin kungiyar NUJ wajan kafa wannan kwamitin
Sannan ya yi ƙira ga NUJ da ta rinƙa shirya taron karawa juna sani ga masu baiwa gwamna Shawara da faraktoci sa akan yadda zasu rinƙa yin rubutu da tafiyar da ofisoshin su dan da yawa wanda gwamnati ke ba mukamai basu da kwarewa wajan rubutun aikin ofis,Idan NUJ ta shirya masu bita zai taimaka gaya wajan aikin gwamnati
A karshe Sakatare kungiyar NUJ na Jihar Zamfara, kwamaret Ibrahim Ahmad Gada ya miƙa godiya da mahalarta taron da fatan kuwa ya koma gida lafiya.
