September 18, 2026

Gwamnatin Katsina Ta Ciri Tuta Wajen Kawo Shirin AGILE a jihar – Maimunatu Mai Kaka.

0

Shugabar makarantar Government Girls Day Secondary school Kafur Maimunatu Mu’azu Mai Kaka ta bayyana hakan a lokacin bude wasu ayyuka da aka gudanar karkashin shirin AGILE a makarantar.

Kamar yadda ta bayyana, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya cancanci a yaba mashi duba da kokarinshi wajen jawo ayyukan shirin na AGILE don amfanin makarantu da dama.

Ya bayyana mahimmancin ayyukan da suka ƙunshi ginawa da gyaran azuzuwan makarantar domin samar yanayin karatu mai kyau.

Maimuna ta ce ɓangaren babban sikandire dan ƙaramar sikandiren makarantar sun samu kimanin naira miliyan 5 da kuma sama da naira miliyan 6.5.

Tunda farko, saida daraktan shiyyar Malumfashi na kwamitin samar da ingantaccen ilimi Bashir Hamza ya gode ma dukkan waɗanda suka halarci taron, tare da bayyana gwamsuwarsu da ayyukan da aka gudanar a makarantar.

A jawabinshi, Dan Galadiman Katsina hakimin Kafur Abdulrahman Rabe ya taya makarantar murna bisa amfana da ayyukan na AGILE, inda ya yi kira suyi amfani da su yadda ya kamata.

Shugaban kwamitin tabbatar da ingantaccen ilimi na makarantar, wanda kuma shi ne Magajin Garin Kafur ya lissafo ayyukan da aka yima makarantar da suka haɗa da gyara azuzuwa da ban-ɗaki, da kuma tona rijiyoyin burtsatse, da dai sauransu.

A tsokacin shugaban kungiyar iyayen ɗaliban makarantar, Abdulsalam Mamman Kafur ya yaba ma shugabar makarantar da malamanta bisa sauke nauyin da aka ɗora masu, tare bada tabbacinsu na taimaka ma makarantar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *