Kotu Ta Tsare Mawallafin Yanar Gizo Bisa Zargin Ɓata Sunan Janar Buratai A Kano.
Wata kotun majistare da ke zamanta a Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Halima A.B. Wali, ta aike da wani mai suna Ibrahim Khalil Danshagamu mawallafi akan yanar gizo mai suna Ibrahim Khalil Danshagamu zuwa gidan yari bisa zargin bata ma tsohon hafsan sojojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya.
Lauyan mai shigar da shigar da kara Hussaini Makari a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaman kotun, ya ce wanda yake karewa ya kalubalanci wanda ake karar ko kuma wani dan jihar Kano cewa su nuna wani gidan mai mallakinsa, shi kau a shirye yake ya janye karar da aka shigar.
Danshagamu, wanda shi ne wanda ake tuhuma, an gurfanar da shi a gaban kotun bisa zarginsa da yada wani faifan bidiyo a shafukansa na sada zumunta, inda ya yi ikirarin cewa wanda ya shigar da karar ya gina gidajen mai sama da 60 a Kano daga cikin kudin sayen makamai.
Bayan watsa faifan bidiyon dai, mai shigar da kara wanda tsohon jakadan Jamhuriyar Benin ne, ya umurci ‘yan sanda da su kamo wanda ake kara domin gudanar da bincike kan ikirarin.
Bayan ‘yan sanda sun kama wanda ake kara, ya musanta zargin da ake masa, kuma Barista Farida Wada ta kai karar a gaban kotun da aka ambata sama.
Lauyan wanda ake kara, S.A Abdullahi, ya roki kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa, abinda kuma alkalin kotun ya nuna rashin amincewarsa akai, tare da bayyana cewa laifin da ake tuhumarsa ya saɓa wa sashi na 371 da 115, saboda laifin zai iya ɗaukar hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari.
Alkalin ya kuma ba da umarnin a aika da wanda ake karar zuwa ga likitan kwakwalwa na jihar don sanin ko yana cikin hankalinsa a lokacin da ya watsa faifan bidiyon, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Sunnews.
