September 18, 2026

Gwamna Buni Ya Gina Cibiyoyin Kiwon Lafiya Matakin Farko 138 A Jihar Yobe

0

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a ranar Talata ya ƙaddamar da sabbin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko (PHCs) guda 138 waɗanda gwamnatin jihar ta sake gyarawa a ƙananan hukumomi 17 a jihar.

A bikin buɗe sabbin cibiyoyin, wanda ya gudana a cibiyar kula da lafiya a matakin farko na unguwar Gwange da ke Damaturu, Gwamna Buni ya ce sake farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiyar a matakin farko ya zama dole sakamakon yadda mayaƙan Boko Haram suka lalata, al’amarin da ya haɗa da gine-ginen jama’a, makarantu, turaku da cibiyoyin wutar lantarki, da makamantan su waɗanda yan ta’addan suka ɓarnata a jihar.

Gwamnan ya ƙara da cewa, gwamnatin sa ta ƙuduri aniyar kawo sauyi mai ma’ana a fannin kiwon lafiya domin inganta sha’anin kiwon lafiya a faɗin jihar.

A hannu guda kuma, Buni ya sanar da mahalarta taron cewa gwamnatinsa ta yi nasarar kammala gine-gine da gyara cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 138 a cikin cibiyoyi 178 waɗanda ya ɗauki alƙawarin samarwa a faɗin jihar Yobe.

Da yake buxe cibiyoyin, Gwamna Buni ya ce, “Wanda domin hakan ne, mun zo nan a yau (Talata) don ƙaddamar da cibiyar kula da lafiya a matakin farko a unguwar Gwange.” in ji shi.

Gwamnan ya ƙara da cewa, ko shakka babu cibiyoyin za su taimaka wajen inganta harkokin kiwon lafiyar al’ummar jihar Yobe, musamman mata da ƙananan yara, tare da bunƙasa ayyukan jinya.

Ya ce, “Akwai cibiyoyin kiwon lafiya guda 8 waɗanda muka inganta su tare da ɗaga darajarsu zuwa manyan asibitoci, a garuruwan Bara, Buni- Gari, Babbangida, Yunusari, Yusufari, Jaji-Maji, Machina, da asibitin Malam Baba da ke garin Nguru.”

Har wala yau kuma, Gwamna Buni ya ce gwamnatinsa ta ɗaga darajar manyan asibitoci huɗu zuwa Asibitocin ƙwararru a garuruwan Buni- Yadi, Gashua, Geidam, da Potiskum domin inganta harkokin kiwon lafiya zuwa matakin gaba a jihar.

Yayin da ya ƙara da cewa, “Ya na da mahimmanci a lura cewa ɗaya daga cikin manyan manufofin gwamnatinmu shi ne inganta harkokin kiwon lafiya don rage yawan mace-mace tare da daƙile cututtuka masu yaɗuwa, da kuma cimma muradun ƙarni wanda ƙasashen duniya suka sanya a gaba, wanda ya ƙunshi samar da ingantaciyar lafiya ga al’umma.”

Gwamnan ya ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen yunƙurin cimma nasarar da ƙasashen duniya suka ƙudurta a fannin bunƙasa kiwon lafiya (UHC) haɗi da sauran manufofin ci gaban ƙarni mai ɗorewa.

A gefe guda kuma, Gwamna Buni ya ƙaddamar da sabbin motocin ɗaukar majinyata (masu taya uku) 88 domin daukar mata masu juna- biyu a faɗin jihar.

Ya ce “gwamnatinsa ta ƙaddamar da motocin domin yankunan karkara wanda hakan zai rage jinkirin kai wa ga cibiyoyi da asibitoci don ceton rai, wanda hakan yasa gwamnatin ta sayo tare da rarraba waɗannan motocin ɗaukar majinyata 88 don su rinƙa jigilar mata masu haihuwa da sauran maras lafiya.”

A jawabin, Kwamishinan Kiwon Lafiya na jihar Yobe, Dokta Muhammad Lawan Gana, ya ce ayyukan gine-ginen da gyare-gyaren cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ko shakka babu zai zaburar da inganta aikin ma’aikatan lafiya da samun damar yin ayyukan ƙwararru a kowane lokaci.

A jawabin maraba wanda Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko na jihar Yobe, Dakta Babagana Kundi Machina, ya ce waɗannan ayyuka suna daga cikin muhimman alƙawuran da Gwamna Mai Mala Buni ya ɗauka tun bayan rantsar dashi a matsayin gwamna; na ƙarfafa hukumar kula da lafiya a matakin farko da kuma tabbatar da samar da aƙalla cibiya ɗaya a kowace gunduma (PHCC) a gundumomi 178 a faɗin jihar Yobe.

Machina ya ce wannan nasara abin a yaba ce, ya ƙara da cewa bisa ga wannan ƙudurin, gwamnati ta na samun goyon baya da haɗin gwiwar qungiyoyi daban-daban kamar su Multi Sectoral Crises Recovery Projects (MCRP), United Nations Development Programme (UNDP), Plan International, NNPC/Cheron/Shell Petroleum a fannin inganta kiwon lafiya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *