Shugaban Najeriya Dana Jamhuriyar Nijar Za Su Buɗe Gasar Karatun Al’kur’ani Karo Na 37 A Zamfara Yau Juma’a.
Daga Hussaini Ibrahim
A wannan Juma’ar 16/12/2022, Shugaban Kasa Muhammad Buhari da takawaran sa na Jamhuriyar Nijar Muhammad Bazun za su buɗe gasar karatun Al’kur’ani Mai tsaki karo na talatatin da bakwai da Jami’ar Usman Danfodiyo ke shiryawa da gabatarwa kowace shekara.
Shugaban Kwamitin gasar, kuma kwamishinan watsa labarai na Jihar Zamfara Ibrahim Magaji Dosara ne ya bayyana hakan ta bakin wakilinsa mai ba gwamna Matawale shawara akan kafafen watsa labarai da sadarwa Zailani Bappa.
Dosara ya bayyana cewa, shugaban Najeriya dana Nijar ne za su jagoranci bude gasar, sai kuma gwamnan Borno Baba Gana Umara Zulum ne shugaban taron, yayinda mai Martaba Sarkin Musulmi da Shehun Barno ne iyayen taron.
Kuma a gasar ta tsawon mako guda, za a tantance hazikan da za su wakilci kasar nan zuwa gasar karatun ta duniya da za a gudanar a kasa Sadiya.
Akan haka ne Kwamitin gasar ke neman goyan bayan al’ummar jihar Zamfara domin ganin an yi taron lafiya an kammala lafiya.
