Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Hakimin Bakori -Masarautar Katsina
A jiya Laraba ne masarautar Katsina ta bada sanarwar dakatar da Hakimin Bakori Alhaji Idris Sule Idris bisa wani zargi da ba a bayyana ba.
Sanarwar wanda Sarkin tsaftan Sarkin Katsina Alhaji Sule Mamman Dee ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a Katsina, ba ta yi ƙarin haske ba akan zargin da ake yi masa.
Sai dai sanarwar ta ce ana gudanar da bincike akan Hakimin Bakori Alhaji Idris Sule Idris, daga masarautar Katsina.
Ya zuwa yanzu dai wata majiya daga fadar Sarkin Katsina na cewa akwai wasu Zarge-Zarge da ake yi dakataccen Hakimin da tasa masarautar ta dakatar da shi.
