Babu Shinkafa da Wake a Zaɓe Mai Zuwa APC Sak Za a yi Cewar Tsohon Gwamna Yari
Daga Hussaini Ibrahim
Dantakarar Sanata a shiyar Zamfara ta Yamma,Kuma Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Hon Abdulaziz Yari Abubakar, tanbayar wa magoya bayan sa da su zabi Jamiyyar APC tundaga sama har Kasa a Zabe Mai zuwa ,ya Karyata zargin da wasu shedanu ke masa na yin wake da shinkafa a Zabe Mai zuwa ,inda ya tabbatar da cewa, duk mutanan sa na cikin Kananan hukumomin goma sha hudo da ke Jihar ,sun aminta da zaben Jam’iyyar APC tundaga sama harkasa.dan su Kai tsaye suke Siyasar su .
Hon Abdulaziz Yari, ya tanbayar da hakan a lokacin da dubban magoya bayan jam’iyyar APC suka tarbe shi a mahaifarsa ,Talatan Mafara dan Fara tattaunawa da dukkan magoya bayan sa da fadin jihar ta zamfara.akan yadda zasu tunkari yakin zaben da zai gudana a shekara Mai zuwa .
Yari, Ya shawarci dukkan magoya bayan jam’iyyar APC a fadin jihar da su tabbatar da goyon bayansu ga dukkan ‘yan takarar da za su fafata a zaben 2023 tun daga shugaban kasa har zuwa kansiloli, da fatan samun nasara.Inji Tsohon Gwamna.
“Mun samu labarin cewa wasu ‘yan siyasa marasa kishin jam’iyyar sun amshi kwangilar domin yiwa Jamiyyar APC zagon kasa a Zabe mai zuwa da yarda Allah ba zasu kai gaciba ,Inji Yari.
Tsohon Gwamnan ya shirya tsaf domin kaddamar da yakin neman zabensa na Sanata a shiyyar Zamfara ta yamma da ta kunshi kananan hukumomin Gummi, Bukkuyum, Anka, Maradun, Bakura da Talata Mafara.domin ganawa da masu rusa da tsaki dan ganin sun samu nasara a Zabe Mai.
