September 18, 2026

Maida ‘Yan Hijra Gidajansu a Duba Wannan Lamarin.

0

Daga Mu’azu Hardawa

Kokarin mayar da ‘yan gudun hijra garuruwan su na asali abin dubawa ne saboda idan ba an yi dace ba, sai bata gari su cigaba da samun matasan da za su horas a matsayin ‘yan bindigarsu, bisa binciken da ya gudanar

A cewarsa ko baya an sha mayar da mutane amma rashin gamsuwa da yanayin da ake ciki a garuruwansu kan sake dawowa ko ‘yan bindiga su sake korarsu kasashen makwabta.

Haka ya sha faruwa hatta jiragen yaki na gwammnati bisa kuskure suna jefa bama bamai a kan mutane da suke zaune a irin wadannan wuraren.

Ya kamata gwamnati ta dubi lamarin so sai saboda hatta tsakanin Damaturu zuwa Gamdu da Jakana da Auno da Mainok da Benisheikh yawanci suna zaune cikin dar dar saboda kowa ya sani ana kallon ‘yan bindiga suna tare hanya suna kwashe mutane suna shiga daji da su.

“Ni ina ga mazauna.yankunan Doron Baga da Kukawa da Gamboru da Gwaza da Damasak da sauransu za su iya fuskantar wannan matsala idan har ba a dauki matakin gaggawa ba”

Ya kamata ayi bincike so sai don kada ayi kitso da kwarkwata a kai bayin Allah ga hatsari. Saboda irin wadannan wurare noma da kasuwanci da kiwo basa yiwuwa, mutane kuma baza su zauna da yunwa ba, dole a c gaba da taimaka musu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *