‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda 3 A Enugu.
An kashe ‘yan sanda uku, yayinda 1 ya bace bayan da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta kan wata motar sintiri da ke tafiya a Enugu.
Harin ya faru ne a daren ranar Laraba a babban Chime Avenue na New Haven a cikin birnin Enugu.
Shedun gani da ido sun fadi ma majiyar Popular News Hausa ta ait.live cewa, kwatsam ‘yan bindigar da suka kai harin a cikin wata mota kirar Lexus SUV, sun bude wuta kan motar ‘yan sandan da ke sintiri, inda suka kashe ‘yan sanda uku.
Bayanai da ba a tabbatar da su ba sun ce, har yanzu ba a ga dan sanda na hudu ba har a lokacin rubuta wannan rahoto.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe wanda ya tabbatar da harin, ya ce ana ci gaba da neman maharan.
