September 18, 2026

HON. Salisu Iro Isansi Wakilin Najeriya…!

0

Kamar yadda kowa ya sani ilmi shine gaba da ke yi wa mai shi jagora domin zuwa wani mataki da ko a mafarki bai yi tunani Ba.

Sannu a hankali wannan sifa tana ƙara bayyana a fuskar ɗaya tamkar da shida ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya.

Hon. Salisu Iro Isansi ya zama wakilin Najeriya ba wai ƙaramar hukumar Katsina ba, inda bayanai suka tabbatar shine jagoran wata tawaga ta musamman domin wakilcn Najeriya akan wasu batutuwa dai suka shafi ƙasar baƙi ɗaya.

Haka ta sa kullum sai na yi wa mutanen Katsina ta tsakiya jaje akan abinda ke shirin samun su, amma har gobe suna da sauran dama wace za su iya fidda kansu idan suna so, idan lokacin yaƙin neman zaɓe ya yi za mu riƙa yin bayani akan irin mutumin da ya kamata jama’ar Katsina su zaɓa.

Yanzu haka dai sun kai ziyara Ƙasar Iran domin tattauna mahimman batutuwa da suka shafi ƙasashen guda biyu musamman abinda ya shafi tattalin arziki, tsaro, da dangantakar diflomasiyya, yadda za a tafi tare.

Irin wannan mutumin ne ake neman rasawa a ƙaramar hukumar Katsina saboda san rai da rashin girmama ilimi da kuma aiki da shi, wannan shi ake cewa sakin na hannu kamun marar inganci, inama inama?

Idan za a yi tunawa a makon da ya gabata ne ministan harkokin waje na Najeriya Geoffrey Onyeama ya kai wata ziyara ƙasar Iran domin kulla yarjejeniya ciki harda sha’anin tsaro da tattalin arziki da harkokin man fetur inda ƙasar Iran zata gina wa Najeriya matatun man fetur

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *