An Daure Lebura Watanni 10 Saboda Satar Murfin Kofa.
A wannan Litinin din ne wata kotu dake Dei-Dei a Abuja ta yanke wa wani lebura mai suna Umar Adamu dan shekaru 20 hukuncin daurin watanni goma a gidan yari bisa samunsa da laifin satar furom din kofofi da darajar kudinsu ya kai naira 45,000, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.
Adamu, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, ana tuhumarsa da hada baki, aikata laifuka da kuma sata.
Sai dai alkalin kotun Malam Sulyman Ola, ya baiwa Adamu zabin tarar naira N30,000.
Ola ya umarci mai laifin da ya biya Naira 30,000 a matsayin tara.
Tun da farko Adamu, ya amsa laifinsa kuma ya roki kotun da ta yi masa sassauci.
Lauyan masu shigar da karar Chinedu Ogada ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 28 ga watan Yuli.
Ogada ya ce wanda ya kai karar Nurudeen Dan Musa dake kauyen Jahi Abuja, ya kai karar ofishin ‘yan sanda na Mabushi a ranar.
Ogade ya ce wanda aka yankewa hukuncin da kuma wani mutum daya da ake cema ‘Yellow’ da bai zo hannu ba har yanzu, sun hada baki ne suka shiga shagon mai karar dake kauyen Jahi.
Ya ce mai laifin ya saci furom din kofofi uku.
Mai gabatar da kara ya ce yayin binciken ‘yan sanda sun samu nasarar kwato furom din kofa daya daga hannun wanda aka yankewa hukuncin, kuma duk kokarin da aka yi na kwato sauran ya ci tura.
Ogada ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 97, 348 dana 287 na kundin laifuffuka.
