Buhari Ya Cika Alkawari Na Sakin Jolly Da Dariye
An sallamo Tsofaffin Gwamnoni guda biyu da Buhari Ya yafe musu laifin badaƙala da dukiyar al’umma.
A yau ne Litinin ne aka sallamo tsohon Gwamnan Jihar Pilato, Mista Joshua Dariye da takwaransa na Jihar Taraba, Mista Jolly Nyame daga gidan gyaran hali na Kuje da ke Birnin Tarayya Abuja.
Sallamar tasu ta biyo bayan afuwar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya musu bayan da kotu da kama su da laifin badaƙala da dukiyar al’ummar Jihohin su a lokacin da suke kan mulki.
📷: Jaridar Vanguard
