Masu Matsala Akan Katin Zaben Su Je INEC Ta Gyara Masu — Musa Mahuta.
Babban sakataren sashen fansho da bada na jihar Katsina ya hori matasan da suka cika shekaru 18 da haihuwa da cewa su mallaki katin jefa kuri’a.
Musa Rabi’u Mahuta ya fadi hakan ne a lokacin da yake duba aikin raba katin zabe dake gudana a karamar hukumar Danmusa.
Babban sakataren wanda shi ne shugaban kwamitin sanya akan rijistar katin zabe a yankin, ya yi kira ga masu matsala ga katin su da su je hukumar ta gyara masu.
A lokacin duba aikin dai babban sakataren ya samu rakiyar shugaban karamar hukumar Dandume Ya’u Noa da sauran yan kwamitin shi, kuma sun duba aikin rijista dake gudana a Dandume A da B, Dantankari, Magaji Wando, da dai sauransu.
Ya ce kwamitin zai ziyarci dukkan mazabu 11 dake cikin karamar hukumar ta Dandume don ganin yadda suke aikin su.
