September 18, 2026

Shiga Lungu Da Sako Na Jami’an INEC Zai Taimaka Wurin Ganin Kowa Ya Samu Katin Zabe — Sanusi Dangi.

0

Shugaban karamar hukumar Danmusa ya bukaci jami’an hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC reshen karamar hukumar Danmusa da cewa su zagaya lungu da saƙon karamar hukumar domin yima wanda basu da katin zabe rijistar samun katin.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanar da shugaban karamar hukumar Danmusa Sanusi Abbas Dangi ya fitar.

Kamar yadda ya bayyana hakan zai ƙara taimakawa wurin ganin kowa ya mallaki katin zaben.

Mazaɓun da yake san a zagaya a karamar hukumar Danmusa don yi masu rijistar dai sun hada: Mara, Dan’alkima, Maidabino, Dandire, Dandire B, Yantumaki A, Maidabino B, Danmusa B, da dai sauransu.

Idan dai ba a manta ba, kwana 2 da suka gabata shugaban karamar hukumar ya yi kira ga al’ummomin karamar hukumar da cewa su fito su mallaki katin zaben don samun damar zabar shugabanni na gari.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *