November 19, 2026

Wasu Yan Bindiga Sun Kai Ma Jami’a Hari A jihar Cross River.

0

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata daliba dake shekarar karshe, tare da raunata wasu da dama a lokacin da suka kai ma wata jami’a mai zaman kanta hari da ake cewa Arthur Javis dake Akpabuyo a jihar Cross River a Kudu maso Kudancin Najeriya.

A martanin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan ya bayar, ya tura jami’an dake yaki da ‘yan daba, masu garkuwa da mutane da sauran laifuka zuwa jami’ar don don shawo kan lamarin, tare da kubutar da wadda akai garkuwa da ita, inji majiyar Popular News Hausa ta AIT.

Harin da aka kai a jami’ar Arthur Javis mai zaman kanta dake jihar Cross River ya kasance ne a daidai lokacin da ake fama da rashin wutar lantarki, inda masu garkuwan da mutane ke amfani da wannan damar wurin yin garkuwa da mutane.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *