Ɗan Shekaru 21 Ne Ya Ba Ɗiyar Ekweremadu Koda, Ba Ɗan Shekaru 15 Ba – Kotun Burtaniya.
Wata kotun majistare da ke Westminster a kasar Birtaniya ta yanke hukuncin cewa David Nwamini Ukpo, wanda ake zargi da bayar da tallafin koda ga diyar Sanata Ike Ekweremadu, dan shekara 21 ne ba shekara 15 ba kamar yadda ake yadawa.
Ekweremadu da matarsa sun gurfana a gaban kotun a yau Alhamis, inda suka ki amsa laifin da ake tuhumarsu da su na hada-hadar sassan jiki, yayin da aka mayar da shari’ar zuwa kotun manyan laifuka ta tsakiya tare da dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Agusta.
An kuma bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan yari har zuwa lokacin da aka dage zaman.
Ba za a sake mayar da shari’ar zuwa Najeriya ba kamar yadda za a saurari shari’ar a babbar kotun manyan laifuka.
Wasu daga cikin ‘yan majalisar dattawa dana wakilai daga Najeriya sun halarci zaman kotun, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar The Nation.
Tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa Eyinnanya Abaribe; tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark; Tsohon karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba da kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje, Adamu Bulkachuwa da wasu fitattun ‘yan Najeriya na cikin wadanda suka halarci zaman.
