September 19, 2026

Harin Kuje: Ba A San Inda DCP Abba Kyari, Dariye Da Nyame Suke Ba.

0

Akwai yiyyuwar wasu manyan fursunoni dake gidan yarin Kuje na Abuja sun tsere bayanda wasu yan bindiga suka kai hari a daren ranar Talata.

Hare-haren da suka dauki tsawon yan sa’o’i, an ce jami’an soji da masu gadin gidan yarin dake bakin aiki sun nuna masu turjiya.

Majiyoyi sun ce mataimakin kwamishinan ‘yan sandan DCP Abba Kyari da mutanensa dake wurin akwai yiyyuwar sun tsere.

‘Yan bindigar dai sun kai hari da abubuwa masu fashewa a cibiyar a daren ranar Talata.

Shi ma tsohon gwamnan jihar Plateau Joshua Dariye da takwaransa na Taraba Jolly Nyame da majalisar jihohi ta yi wa afuwa an ce suna cikin gidan yarin.

Har ya zuwa lokacin kai wannan harin dai gwamnatin tarayya ba ta sake su ba.

Majiyoyi a ginin yarin sun shaidawa majiyar Popular News Hausa ta jaridar The Nation cewa baya ga manyan fursunonin, wasu ‘yan ta’adda da sauran masu laifi sun tsere a lokacin.

Ba a samu wayar salular jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da gidajen yarin Najeriya, Francis Enobore na babban birnin tarayya Abuja ba a lokacin da aka neme shi saboda wayoyinshi na kashe a cewar majiyar Popular News Hausa ta The Nation.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *