September 18, 2026

An Saki Kudin Masu Dafa Abincin Yan Makaranta.

0

Mai ba gwamnan jihar Katsina shawara akan tallafama rayuwar al’umma ya ce gwamnatin tarayya ta saki kudaden masu dafa abinci na shirin ciyar da yara yan makaranta a jihar Katsina.

Abdulkadir Mamman Nasir ya bayyana cewa an saki kudin ne da nufin ciyar da yara yan makarantar firamare a tsawon wata daya.

Mai ba gwamnan shawara ya bukaci masu dafa abinci da su tsaida aikin dafa abincin har nan da zuwa bayan salla domin ci gaba.

Ya kuma yi kira ga masu dafa abincin da su ji tsoran Allah tare da yin aikin dafa abincin daidai yadda aka kulla alkawali da su.

Abdulkadir Mamman Nasir ya yaba ma gwamna Aminu Bello Masari da shugaban kasar Muhammad Buhari bisa nuna damuwarsu wurin bunkasa rayuwar masu karamin karfi.

Bayanin hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na sashen tallafa ma al’umma Abubakar Mamuda ya sanya ma hannu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *